<?xml version="1.0" encoding="UTF-8"?><song><hymn_number>81</hymn_number>
<title>Ku Ji Muryar Annabci Kuwa, da Allah Ya Faɗa LW81</title>
<lyrics>[V1]
 1) Ku ji muryar annabci kuwa, da Allah ya faɗa.
 Ishaya ne ya ambata abin al'ajabi.

[V2]
 2) Ga shi an haifi yaro dai, mu aka bai wa Ɗa.
 Sunansa. kuwa Al'ajabi, kuma Mai Shawara.

[V3]
 3) Allah mai iko duka kuwa, Madauwamin Uba,
 Sarkin Salama, mulkinsa ba shi da iyaka.

[V4]
 4) A bisa kursiyin Dawuda, da bisa mulkinsa,
 Zai kafa shi kan shari'a da kuma gaskiya.

[V5]
 5) Wannan, Allah mai runduna da himmarsa zai yi.
 Maganarsa zai cika ta, alkawari ya yi.

[V6]
 6) Yau cikin birnin Dawuda fa aka haifi Yesu.
 Mu tafi can sakarkari, sujada za mu yi.</lyrics>
</song>